Kuskure Ne Rufe Titi A Yayin Sallar Juma’a, Cewar Sheik Qaribullahi Nasiru Kabara
DAGA Imam Indabawa Aliyu
Babban Malamin addinin musulunci a Najeriya kuma Khalifan Kadiriyya na Afirka ya caccaki masallatan juma’an da suke rufe hanya a yayin sallar juma’a da cewa kuskure ne wanda Annabi Sallallahu Alaihi Wa sallam ya yi hani da shi.
A yayin karatun littafin hadisi na “Attajul Jami’u Lil’usul Fi Ahaadisir Rasul” da yake gudana a kowanne mako shehin Malamin ya karanto hadisin da ya yi hani da yin salla a wurare bakwai wanda cikinsu har da tsakiyar hanya.
“Ba adalci ba ne rufe hanya a yayin sallar juma’a da wasu masallatai ke yi. Akwai masu lalura, akwai mara lafiya ko mace mai haihuwa, ko wanda suka yi hadari da za a kai asibiti.
wanda rufe hanyar ke sanya su cikin mummunan yanayi. Ya kamata ko me za a yi kar a rufe hanya baki daya a dinga rage hanya ko yaya take. Wani shi ma limami ne zai je ya ba da sallar juma’a mutane na jiransa, amma an tare masa hanya. Wannan ba adalcin musulunci ba ne.” A cewar Khalifan Kadiriyya Shaikh Qaribullahi Amirul Ansar.