BIDIYO: Yadda Mahaifiyar Deborah Samuel Ta Fadi Wani Al’amari Da Ya Faru Kafin Mutuwar Deborah Samuel
Alheri Emmanuel, mahaiflyar Deborah Samuel, Dalibar kwalejin ilimi ta tunawa da Shehu Shagari dake Sakkwato, wacce aka kashe bisa zargin batanci, ta bayyana yadda labarin kisan diyarta ya zo kunnenta.
Alheri ta bayyana halin da ta shiga ne a wata hira da sashin Hausa na BBC, inda ta ce ta samu labarin kashe diyarta ne ta bakin kawar Deborah.
Mahaifiyar, wacce ta fashe da kuka yayin da take hirar, ta bayyana cewa ba zata taba mance wa da wannan ranar ba a rayuwarta.
kalli bidiyan tattaunawar da bbc hausa sukayi da alheri
A Cewar daily trust alheri ta bayyana cewa ‘A ranar da wannan mummunan labarin ya faru naji tamkar an soke ni, daya daga cikin kawayenta ta kira ni ta wayar salula. Tun kamin ta fada mun naji suna kuka, ta ce Mama sun yi alkawarin sai sun kashe Deborah.”
“Bayan wani lokaci sai makotan mu da yan uwa suka fara zuwa jajanta mana. Wata kawarta ta daban ta sake kira na, ta ce Mama sun kashe Deborah.”
Kisan Deborah ya haddasa zazzafar muhawara a sassan kasar nan baki daya, inda wasu yan Najeriya suka yi kira ga gwamnatin tarayya ta binciko wadan da suka aikata wannan babban laifin.
Matasa kuma daliban makarantar kwalejin llimi ta Shehu Shagari sun kashe Deborah ne bayan ta yi kalamai munana har da zagi ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).
Bayan faruwar wannan lamari, hukumar yan sanda a Sakkwato ta sanar da cewa ta kama wasu da take zargin suna da hannu a kisan, lamarin ya haifar da zanga-zanga a sassan jihar Sakkawato.
masu sauraranmu a koda yaushe bayan kun karanta wannan labarin zamu so karben ra’atoyinku a sahen mu na tsokaci sannan muna da bukatar da ku danna mana alamar kararrawar sanarwa.