SUBHANALLAHI: Ku Kalli Yadda Akai Bukin baiwa ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan Ado Aliero sarauta a Zamfara
Cincirindon al’umma ne su ka halarta, yayin da a ka yi wani gagarumin biki a garin Tsafe, bayan da Sarkin Ƴandoton Daji a Jihar Zamfara, Aliyu Marafa ya naɗa wani shugaban ƴan fashin daji mai suna Adamu Aliero Yankuzo, wanda aka fi sani da Ado Alero, a matsayin Sarkin Fulanin masarautar.
Bikin dai ya zo ne bayan shekara biyu da ƴan sanda suka bayyana cewa ana neman Aliero ruwa a jallo, tare da sanya ladan Naira miliyan 5 ga duk wanda ya gano shi.
Alero shi ne shugaban ɗaya daga cikin kungiyoyin ƴan ta’adda da ke da alhakin kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane a Kananan Hukumomin jihohin Zamfara da Katsina.
Wani ɗan jarida mai suna Abdul Balarabe ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a jiya Asabar, inda a ka riƙa shagalin bikin naɗin sarautar da babura.
“Daga karshe, an naɗa ƙasurgumin ɗan fashin nan mai suna Ado Aleru a matsayin Sarkin Fulani (Sarkin Fulani) na masarautar Ƴandoton Daji a jihar Zamfara. Wanda ya faru da misalin karfe 3:30 na yammacin yau Asabar 16 ga Yuli, 2022.
“Ado Aleru shi ne shugaban ƴan bindigar da ke addabar al’ummar Katsina da Zamfara.
“Rundunar ƴan sandan Katsina ta bayyana cewa tana neman sa a shekarar 2019 tare da ladan Naira miliyan 5 a kansa,” Balarabe ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter, @abdul_donjay.
A watan Yunin 2020, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina, Sanusi Buba, yayin da yake bayyana Alero a matsayin wanda a ke nema ruwa a jallo, ya ce: “Rundunar ta sanar da neman Adamu Aliero, mai shekaru 45, na kauyen Yankuzo na karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Ƴandoton Daji na ɗaya daga cikin sabbin masarautu biyu da gwamnatin jihar ta kafa a watan Mayu tare da Bazai.
Sai dai wasu majiyoyi sun ce an yanke shawarar baiwa shugaban ‘yan ta’addan sarautar gargajiyar ne da nufin samar da dawwamammen zaman lafiya a yankin, bayan munanan hare-haren da kungiyar Alero ta kai.
Da DAILY NIGERIAN ta tuntubi kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar Zamfara, Mamman Tsafe, ya ƙi cewa komai kan lamarin.
Ƙoƙarin yin magana da kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara, Ibrahim Dosara bai yi nasara ba saboda bai dauki waya ba mai kuma bada amsar sakon waya da da aka aike masa ba.