Tarihin Isaac Idahosa, Mutumin Da Kwankwaso Ya Zaba A Matsayin Mataimakinsa
Dan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zaɓi Fasto Bishop Isaac Idahosa a matsayin mataimakinsa a zaɓen 2023.
Wata sanarwa da jam’iyyar NNPP ta fitar ranar Alhamis ce ta bayyana Idahosa a matsayin wanda zai yi wa tsohon gwamnan Kano mataimaki.
An jima ana dakon wanda Kwankwaso zai zaɓa bayan rushewar ƙawance tsakaninsa da ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi.
Isaac Idahosa ne na uku a wurin mahaifinsa wanda ke da ƴaƴa shida.
Mista Idahosa dan asalin Jihar Edo ne da ke Kudu maso Kudancin Najeriya. Ko da yake an haife shi a Minna da ke Jihar Neja a Arewacin kasar, inda Musulmi suka fi yawa.
Ya yi karatun boko a can kuma ya samu tallafin karatu har zuwa Jami’a a jihar Neja.
Ya auri matarsa mai suna Christie Idahosa, kuma sun haifi ‘ya’ya biyu tare, Christabell da Osagie.
Faston, wanda fitaccen mawakin bushara ne, ya taɓa samun lambar yabo ta Majalisar Dinkin Duniya a matsayin jakadan zaman lafiya, saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban bil adama da zaman lafiya ta hanyar wa’azinsa.
Ya fitar da kundi uku na jerin waƙoƙin bushara a baya.
Bishop Isaac Idahosa shi ne shugaba, kuma babban Fasto na cocin God First Ministry, wadda aka fi sani da Illumination Assembly, da ke Lekki Ajah, a jihar Legas.
Cocin da ya kafa sama da shekaru 25 da suka gabata.
Mabiyan faston na kiransa da suna ‘Prophet Talk Na Do’, wato mai cika aiki.
Idahosa kwararren Injiniya ne, wanda ya sauya ya rungumi wa’azin Kirista daga baya.
Yadda ya zama mataimakin Kwankwaso
Gabanin wannan sanarwa dai an jima ana dakon ganin wanda Sanata Kwankwaso zai zaɓa a matsayin mataimaki duba da cewa manyan jam’iyyun ƙasar sun sanar da nasu.
A baya an so yin gamin-gambiza tsakanin NNPP ta su Kwankwaso da LP ta su Peter Obi don ɗaya ya mara wa ɗaya baya, amma daga baya shirin ya wargaje.
Daf da ƙarewar wa’adin farko na miƙa sunayen mataimaka, Kwankwaso ya mika wa hukumar zaɓen kasar INEC sunan wani lauya dan jihar Legas Barista Ladipo Johnson a matsayin dan takarar riƙo, kafin sauya sunansa a yanzu