Shari’ar Sheikh Abduljabbar: Lawyan wanda ake ƙara ya fice daga kotu bayan zargin Alƙali da rashin adalci.
Aliyu Samba
A safiyar yau ne aka cigaba da sauraren Shari’ar malamin addinin Muslunci Sheikh Abduljabbar Kabara wadda ake gabatarwa a babbar kotun shari’ar Muslunci dake zaman ta a kofar kudu.
Kamar yadda ya gabata a zaman da ya shuɗe, yau kotu zata faɗi matsayin ta akan roƙon da Lawyan wanda ake ƙara yayi, tare da cigaba da tambayoyi ga shedar kariya na daya a shari’ar.
Yayin Zaman na yau, Lawya Dalhatu Shehu Usman wanda yake kare wanda ake ƙara ya roki kotu akan cewa yana son zai yi abinda a Shari’a ake cewa ”No Case Submission”, dogaro da hujjojin da suka gabata a kotu, yana son bijirar da cewa babu wata tuhuma akan wanda ake ƙara.
Saidai lawyoyin da ke gabatar da ƙara sunyi inkari akai tare da bijirar da nasu dalilan na inkarin. A nan ne kotu tayi hukunci bayan nazari na ɗan lokaci akan abin da bangarorin biyu suka bijirar na hujja a gaban kotun.
Alƙali Sarki Yola yayin kwarya-kwaryar hukuncin sa, inda ya ce a wannan gaɓar da ake ta Shari’a, suka akan ingancin Tuhuma kawai ake da damar gabatarwa, amma babu damar shi ‘no case Submission’, ya yanke hukuncin cewa wannan roƙo bazai karɓu ba, kuma ya bada umarnin a cigaba da tambayoyi ga sheda.
Daga tambayoyin da akayi wa shedar, masu gabatar da ƙara sun buƙaci ya bada kwafin ‘Ijazozi’ da ya ambata a zaman da ya gabata cewa ya karɓa daga wajen mahaifin sa Sheikh Nasir Kabara. Wanda ake ƙara ya mika wa kotu wadannan ‘ijazozi’ sannan ya cigaba da amsa tambayoyin da ake masa a kotu.
A yayin gabatar da tambayoyin, lawyan wanda ake ƙara ya miƙe tare da yin suka akan wasu daga tambayoyin da masu gabatar da ƙara suke yi, wanda a cewar sa basu da alaka da shari’ar. Saidai mai Shari’a Alƙali Ibrahim Sarki Yola bai saurari wannan suka ba, ya bada umarnin a cigaba da yin tambayar.
A nan ne lawyan wanda ake ƙara ya bayyana cewa muddin ba za a bar su suyi suka akan tambayoyin ba, to ba buƙatar su cigaba da yin shari’ar a wannan kotu. Ya kara da cewa doka ce ta basu cikakkiyar dama, ba zai zama adalci ba kotu ya hana su abinda doka ta basu dama.
Mai Shari’a bai amince da wannan rokon ba. Ya kuma ce ”a sauka lafiya” a daidai gaɓar da Lawyan wanda ake ƙara yace shi tafiya zai yi muddin ba a bashi damar da yake da ita a doka ba.
Bayan ficewar lawyan daga kotu, mai Shari’a ya dage zaman Shari’ar zuwa 21/7/2022 don cigaba da shari’ar.
A tattaunawar manema labarai da Barista Dalhatu Shehu Usman, ya bayyana cewa wannan kotu ba adalci take yi ba, domin ta dauki matsayin masu gabatar da ƙara ne.
Ya kuma yi zargin cewa Alƙali Ibrahim Sarki Yola ɗalibi ne ga ɗan uwan wanda ake ƙara wato Sheikh Ƙaribullahi Kabara, wanda a cewar Dalhatu, a wajen sa ne aka tsara tambayoyin da ake yi a kotun ga wanda ake ƙara.
Ya kuma bayyana cewa baza su cigaba da yin wannan Shari’a a wannan kotun ba, saboda abinda ya kira rashin adalci daga Alƙalin.