Politics

DA ƊUMI-ƊUMI: Babu Jonathan A Cikin Jerin sunayen ‘Yan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar APC

DA ƊUMI-ƊUMI: Babu Jonathan A Cikin Jerin sunayen ‘Yan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar APC

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba ya cikin jerin sunayen ‘yan takarar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta tantance.

A halin da ake ciki, wata babbar kotun tarayya da ke zama a Yenagoa, jihar Bayelsa a ranar Juma’ar da ta gabata ta bayyana cewa Jonathan ya cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Hamma Adama Dashen ya ce, sauyi na hudu da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasa Jonathan bai shafe shi ba, na hana mataimakan shugabanin da suka gaji shuwagabannin su ci gaba da wa’adi fiye da daya.

Sauyi na huɗu na Kundin Tsarin Mulki na 1999 wanda ya haramtawa mataimakan shugabanin da suka gaji shugabanninsu yin cikakken wa’adi fiye da ɗaya.

Jonathan ya kasance mataimakin shugaban Najeriya a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2010. Ya zama shugaban kasa a watan Mayun 2010 bayan rasuwar shugaba Umaru Musa ‘Yar’Adua kuma ya kammala wa’adin mulki.

Ya lashe zaben shugaban kasa a shekara ta 2011 amma ya sha kaye a yunkurinsa na neman wa’adi na biyu akan karagar mulki a shekarar 2015.

SaharaReporters ta tattaro cewa hukuncin na daya daga cikin shirye-shiryen da kungiyar Aso Rock ke goyon bayan Jonathan domin ganin tsohon shugaban kasar ya karbi mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar a ranar Alhamis din da ta gabata ta ruwaito cewa Jonathan ya mika fom din tsayawa takarar shugaban kasa na Naira miliyan 100 a kwanakin baya ga shugaban jam’iyya mai mulki ta kasa Abdullahi Adamu.

Sai dai ba a ga sunansa ba a cikin jerin sunayen ‘yan takarar shugaban kasa 23 da jam’iyyar APC ta fitar.

Sunayen ‘yan takarar shugaban kasa na tantancewa kamar yadda APC ta lissafa:

1. Chukwuemeja Uwaezuoke Nwajiuba
2. Badaru Abubakar
3. Robert A. Boroffice
4. Uju Ken-Ohanenye
5. Nicholas Felix
6. Nweze David Umahi
7. Ken Nnamani
8. Gbolahan B. Bakare
9. Ibikunle Amosun
10. Ahmed B. Tinubu
11. Ahmad Rufai Sani
12. Chibuike Rotimi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button