News

Hukumar DSS sun kama yan ta’addan Boko Haram biyu da ake zargi da hannu a harin ta’addancin da akai a Jihar Kano

Hukumar DSS sun kama yan ta’addan Boko Haram biyu da ake zargi da hannu a harin ta’addancin da akai a Jihar Kano

Aliyu Samba

Biyo bayan fashewar wani abu da aka ce tukunyar gas ne a unguwar Sabon Gari dake jihar Kano, binciken sirri da hukumar tsaro ta DSS tayi yayi nasarar kama ƴan Boko Haram biyu kwana ɗaya bayan faruwar al’amarin a jihar Kano.

Wata majiya ta sirri ta bayyana mana cewa yan Boko haram biyun da aka kama washegarin faruwar al’amarin sune ake zargi da hannu a fashewar bom din da aka bayyana cewa tukunyar gas ce.

Idan za a iya tunawa, hukumar yan sanda ta bakin Kwamishinan Ƴan Sanda na jihar Kano CP Sama’ila Shu’aibu Dikko fsi sun musanta cewa fashewar bom ne ya faru a Unguwar ta sabon Gari inda ya bayyana cewa tukunyar gas ce ta fashe wacca tayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, sannan kuma sun gano wasu sinadarai (Chemicals) a jarkoki guda 2 a wajen da al’amarin ya faru.

Saidai a wata tattaunawa da gidan talabijin na ‘Arise News’ suka gudanar, Shugaban makarantar Winners Triumph Excel academy, Mista Lennie Ujaja wanda harin ya faru dab da su, ya bayyana cewa wani dan ƙunar baƙin wake ne ya zo ya tashi bom a wajen, an kuma samu wasu shedun gani da ido da suka tabbatar da haka.

Kayayyakin da aka samu tattare da wadanda ake zargin yana karfafar cewa bom ne ya tashi wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 9, domin an kama waɗanda ake zargin da jarkoki masu ɗauke da wasu sinadarai (Chemicals) tare da rasiti da ke nuna cewa sun sayi kayan ne a wajen da al’amarin ya faru a unguwar sabon Gari.

Wadanda ake zargin mutum biyu yan asalin jihar Bauchi ne da kuma jihar Yobe.

Hukumar ta DSS tayi nasarar kwato bindigogi 4 ƙirar AK47, Pistol guda 2, sai kuma silken ƙunar baƙin wake da kuma abubuwan hada bom da ake cewa IED.

Wannan na zuwa makonni kadan bayan ikirarin da Gwamnan jihar Kaduna yayi cewa Yan Ta’addan Boko Haram sun mamaye kananan hukumomi 2 a jihar Kaduna.

A kwanukan nan, hare haren ta’addanci na cigaba da ƙamari a jihohin arewa maso yammacin Najeriya, kuma rahotanni suna bayyana cewa yan ta’addan Boko Haram na balaguro daga arewa maso gabas sakamakon yawaitar hare haren soji akan sansanonin su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button