CIN AMANA: Babban abokin ango ya sace kayan lefen amarya a Kano
Wani babban abokin ango a unguwar Gaida da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano ya shiga gidan ma’auratan ya sace wa amaryar kayan lefe da ya kimar sa ta kai Naira 500,000.
Lamarin ya faru ne mako ɗaya bayan angon ya tare, shi kuma abokin na sa yana da mukullin gidan a hannu, har ma angon ya nemi ya dawo masa da mukullin amma bai dawo da shi ba.
Da ya ke bayani ga manema labarai a Kano, bayan sun cafke abokin angon da a ke zargi da tafka satar a jiya Alhamis, Shugaban ƴan vigilante na unguwar Gaida, Shekarau Ali, ya ce binciken da su ka yi ne ya sanya su ka gano ɓarawon.
A cewar sa, shi angon ya kai musu ƙorafin an tafka masa sata, inda binciken su ya gano cewa ƴan uwan amaryar ne su ka ba wanda a ke zargi da satar mukullin gidan domin ya baiwa angon bayan sun kammala jeren kayan amarya a gidan.
“Da ga nan ango ya nemi ya bashi mukullin amma ya kiya har sai da ya jira sun fita da amaryar, shine ya buɗe gidan ya sace mata kayan lefe, har da ma wasu kayaiyakin abinci.
“Da ga nan ne binciken mu ya nuna mana cewa shi wannan abokin, shine ya ci amana ya tafka wannan sata kuma tuni ya na hannun mu. Idan mun kammala bincike, zamu miƙa shi ga ƴan sanda domin yi masa hukuncin da ya dace,” in ji Ali, wanda a ke wa laƙabi da cinnaka ba ka san na gida ba.
A cewar wanda a ke zargin, sharrin shaiɗan ne ya zuga shi ya ci amanar babban abokin nasa, inda ya roki a yafe masa kuma yai alƙawarin ba zai sake aikata irin wannan laifin ba.
Sai dai kuma ya yi wa angon gori cewa shima ai ya kashe masa sama da Naira dubu 400 a bikin nasa.