Abba Kyari ya musanta zargin laifin safarar hodar ibilis
A yau Litinin ne a ka gurfanar da dakataccen Mataimakin Kwamishinan Ƴan Sanda Abba Kyari tare da wasu mutane shida a Babbar Kotu a Abuja.
Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA ce ta gurfanar da su a bisa tuhumar su da zargin laifin safarar hodar ibilis.
Da a ke karanto masa laifukan sa, Kyari ya musanta laifi na ɗaya, biyu, uku, huɗu da na takwas, inda sauran yan sanda huɗu da suka ake tuhuma su ka musanta laifi na ɗaya, biyu, uku da na huɗu.
Sai dai kuma Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne, waɗanda su ne waɗanda a ke zargi na 6 da na 7, sun amsa laifi na biyar, shida da na bakwai.
Huɗu da ga cikin ƴan sandan, waɗanda su ke sashin rundunar sintirin sirri ta Shelkwatar ƴan sanda, su na cikin ƙarar mai lamba, FHC/ABJ/57/2022, inda a ka bayyana sunayensu da ACP Sunday J. Ubia, ASP Bawa James, Insp. Simon Agirigba and Insp. John Nuhu.
Umeibe alda Ezenwanne su kuma ana zargin su da safarar miyagun ƙwayoyi ne a Filin Jirgin Sama na Kasa da Kasa da ke Akanu Ibiam a Jihar Enugu.
Mai Shari’a Abubakar ya dage zuwa gobe Talata domin sauraron rokon lauya Kyari.