Gwamnatin Nijeriya ta amince da a yi shari’ar Abba Kyari a Amurka
A yau Alhamis, Gwamnatin Taraiya ta amince da buƙatar Ƙasar Amurka ta a maida dakataccen Mataimakin Kwamishinan Ƴan Sanda, DCP Abba Kyari zuwa ƙasar domin gurfanar da shi a gaban kotu a can.
Amurka, a wani rahoto na Hukumar Binciken Sirri, FBA, na tuhumar Kyari ne da hannu a cikin badaƙalar kuɗaɗe da su ka kai dala miliyan 1.1, tare da Ramon Abbas, wanda a ka fi sani da Hushpuppi da wasu mutane 4.
A yanzu haka Kyari na nan a tsare a Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA a kan zargin safarar hodar ibilis.
Ministan Shari’a na Ƙasa, kuma Antoni-Janar na Ƙasa, Abubakar Malami, SAN, ne ya amince da tasa ƙeyar Kyari ɗin zuwa Amurka bayan da ya miƙa buƙatar hakan a gaban Babban Mai Shari’a na Babbar Kotun Taraiya a Abuja.
Takardar miƙa buƙatar, mai lamba FHC/ABJ/CS/249/2022, an shigar da ita ne a bisa dokar yi wa mai laifi Shari’a a kasar waje.
Antoni-Janar ɗin ya yi bayani cewa amincewar ta biyo bayan buƙatar hakan da Amurka ta miƙo wa ta ofishin jakadancin Amurka da ke Nijeriya.