Kotu ta ci tarar KAROTA sakamakon kama masu goyo a babur
Babbar Kotun Jiha da ke Bompai a Jihar Kano ta umarci Hukumar Kula da Sufuri ta Jiha, KAROTA ta biya wasu mutane uku N500,000 kowannensu bayan da hukumar ta kamasu da zargin yin goyo a baburansu.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, watanni 18 ke nan da wasu mutane 9 su ka shigar da KAROTA ƙara a gaban koton, bisa kamasu da suka yi don kawai sun dauko iyalansu a bayan baburansu.
Da ga ƙarshe, a yau Litinin, alkalin ya yanke hukunci cewar hukumar KAROTA ta aikata laifi da ta kama mutanen kuma ta umarceta da ta biya su diyya.
Koton ta umarci a biya mutane ukun farko diyyar N500,000 kowanne kan kamasu da aka yi ba bisa ka’ida ba, sai kuma wata N100,000 kan bata musu lokaci.
Haka kuma ragowar mutane shidan aka hakurkurtar da su tare da tabbatar da anyi musu laifi.
Jimkadan bayan yanke hukuncin ne lauyan wanda ke kare masu korafin Barrister Abdulkareem Kabir Maude ya ce kotu ta tabbatar da cewa kowa zai iya goyo a kan baburinsa.
Ya ce kotu ta yi umarnin a dowowa da wanda aka ci tara kudadensu da aka karba kuma a biya su diyya.
Da ga ƙarshe, Alƙalin kotun, mai shari’a Nasiru Saminu ya ce a yanzu yin goyo a babur ba laifi bane a dokar kasa, matukar ba haya suke yi da baburan ba.
https://youtu.be/t8kgrbi6eGo