Daya Daga Cikin ‘Ya’yan Talakawan Da Kwankwaso Ya Dauki Nauyin Karatunsu A Kano Zuwa Kasar Indiya Ya Yi Zarra, Inda Ya Kammala Da Sakamako Mafi Daraja
Dan Jihar Kano da gidauniyar Kwankwasiyya ta dauki nauyin tafiya karo karatun sa, wato Abubakar Soja ya yi zarra a jami’ar Sangam dake kasar Indiya, inda ya kammala karatunsa na Digiri na biyu a fannin Kimiyyar Adana Bayanai (Masters of Information and Library Science) da sakamako mai daraja (First Class).
Tun lokacin da jagoranmu tsohon Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bullo da tsarin tallafawa dubunnan ‘ya’yan talakawa ta hanyar fitar da su kasashen waje domin su karo karatun.
da yawa daga cikin manya a kasar nan, musamman ma gwamnoni sun soma koyi da tsohon Sanatan, wajen ganin cewa suma sun nuna hubbasa akan rayuwar talakawansu domin sunji dadin mulkin dimokradiyya a karkashin mulkin su.
Wannan tunani bai taba zuwa kai na ba sai dana samu wani labari da yake nuna cewa gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya sha alwashin tallafawa ‘ya’yan talakawa guda 700
Domin su fita su karo karatu a kasashen wajen. Hakan yasa na gane cewa tabbas yana son yabi sahun Kwankwaso ne.
Hakan yasa nake yiwa tsohon Sanata Kwankwaso jinjina akan irin yadda yake fito da sabbin abubuwa wadanda talakawa zasu amfana har wasu shugabannin su yi koyi da wannan abu.
A makon da ya gabata ne dai tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya ya kai ziyara kasar Indiya domin ya nemawa ‘yayan talakawa sama da 300 da gidauniyarshi ta yi alkawarin tallafawa su karo karatu a kasashen waje.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon Sanatan sun kammala yarjejeniya da wata katafariyar jami’a ta kasar ta Indiya akan maganar karatun daliban.