News

Mummunan Tashin Farashin Kayan Abinci A Kudu Na Dada Yin Kamari

Farashin kayan Abinci yayi mummunan tashin da bai tabayi ba a kudan cin Nigeria.

Alummar kudancin nigeria na cigaba da kokawa kan yadda yan Arewa suka hada kai kan qin shigar musu da kayayyakin abinci.

Lamarin da ya jawo hauhawar farashin kayayyakin abincin da suka rage a yankin.

Wanda muddin Yan Arewa basu dakatar da yajin aikin da suka soma na qin kai musu kayan abinci su saya ba Hakan Ka iya shafar kasuwanci dama karya kana nan yan kasuwa.

Jama’a da dama daga yankin na rokon Shugabannin yan kasuwar da suwa Allah su dakatar da yajin aikin nan haka.

A ta bakin shugaban Yan kasuwar safarar kayan abinci ta kasa Dr.Muhammad Tahir. Cewa Yai Muddin ba’a biya su Asarar da sukai ba dakuma diyyar mutanen da aka kashe musu tun daga lokacin fara zanga zangar kawo karshen rundunar yan sandan Sars har izuwa yanzu to kar ma asaka rai da janye yajin aikin da suka soma.

Lamarin da wasu ke ganin ya dace ace sun tsagaita da wannan yajin aikin domin yan kudu su sami saukin tsadar rayuwa.

A inda wasu ke ganin abar yan kudun suma su dan dana kudar su. Ko zasu gane amfanin hausawa a gare su.

Anan muke so daku bayyana mana ra’ayoyin ku kan wannan batun.

Shin kuna goyan bayan kungiyar masu kayan abinci ta Arewa ta janye yajin aikin nan ko kuwa aci gaba

Related Articles

4 Comments

  1. Bama goyan bayan haka,har sai anbiya mana abinda yan uwanmu sukayi asarah,tundaga lokacin rikicin end SAS harzuwa rikicin kabilanci DA sukayi mana.sabuda my nan bauchi muna zaune lafiya DA kowa bame tsangwaman wani,har arewa yakanfi musu garuruwan su dadi,muna zaman lafiya DA kowa sai dai Dan rikicin makobci DA makobci,kuma ya kamata suyan kudu Susan cewa kasa daya muke.bai kamata ace muna fada ah tsakanin muba. Allah ya Kara hadakan mu yan Nigeria. Abiya mana diyan yan uwanmu tukun.

  2. A gaskiya Muna jin dadin wannan doka ta Hana shiga da kayan masarufi zuwa kudancin Nigeria saboda su gane cewa mu al-ummar hausa munada mahimnanci sosai

  3. Muna goyon bayan wannan lamari, kuma muna fatar Allah yasa yayi tasiri.Amma in an chiza ahura domin akwai mutanenmu achan cikinsu kuma mafiya yawansu talakawa ne.Allah yakyauta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button