An gurfanar da matar Abdulmalik Tanko da ya kashe Hanifa a kotu
Rundunar ƴan sandan Jihar Kano, a jiya Alhamis ta gurfanar da Jamila Muhammad Sani, matar Abdulmalik Tanko, wanda a ke zargi da yin garkuwa da kuma kashe Hanifa Abubakar a jihar.
An gurfanar da ita a gaban Kotun Majistiri mai Lamba 12, ƙarƙashin mai shari’a Muhammad Jibril da ke zamanta a gidan Murtala.
Mai gabatar da ƙara, kuma lauyan gwamnati, Lamido Abba Soron Ɗinki tare da rakiyar Barista Maryam Jibril da Barista Hafsat Kabir da kuma Barista Hafsat Adda’u, ya roƙi kotu da ta karantowa wadda ake tuhumar.
Jami’in kotun ya karanto mata tuhumar, wadda ta ƙunshi ɓoye da kuma tanadar da wajen da aka sace yarinyar, wato Hanifa, har ta kwashe kwanaki biyar a gidanta.
Sai dai kuma ta musanta zargin nan take, ta kuma nemi damar yin magana, amma kotu ba ta amince da bukatar ta ba.
Da ga nan ne sai mai gabatar da ƙara ya roki kotu da ta basu wata ranar, domin sake gabatar da ita, yayin da kotun ta sanya ranar 2/2/2022, ta kuma umarci a mayar da ita wajen jami’an tsaro ba gidan gyaran hali ba.
https://youtu.be/wtH0NPH7TAw