News

BIDIYO: Ko da ba a kama ni ba, na yi niyyar fallasa kaina, in ji wanda ya kashe Hanifa

Ko da ba a kama ni ba, na yi niyyar fallasa kaina, in ji wanda ya kashe Hanifa

Abdulmalik Tanko, mamallakin makarantar Noble Kids Comprehensive College, wanda ya sace da kuma kashe Hanifa Abubakar, ya ce dama can ya yi niyyar fitowa ya amsa laifin kisan nata ko da ma jami’an tsaro ba su kama shi ba.

A makon da ya gabata ne dai Tanko ya shiga hannun jami’an tsaro yayin da ya ke yunƙurin karɓar cikon naira miliyan 6 na kuɗin fansar garkuwa da Hanifa da ya yi, yarinya ƴar shekara 5 da ke karatu a makarantar ta sa.

Da ya ke zantawa da Sashen Hausa na VOA, Tanko ya ce ko da ma ba a kama shi an kai shi kotu ba, to ya yi niyyar ya fito ya nuna kan sa sabo da yadda lamarin ke damun sa.

“Ko da ma kafin a kawo ni kotu, hali ne na tashin hankali na ke ciki. Duk wanda ya san ni a baya zai san haka.

“Shi wannan al’amari ne wanda dama ba wanda zai ji daɗin shi ai. Ko da a ce ta na da ɗa ko ba ta da ɗa ai Musulmi ne mu. Su ma na tabbatar ai ba za su ji daɗi ba.

“Tun kafin ma a kawo ni kotu, dama na yanke a raina cewa dole na fito na yi magana.

“Tunda ka ga na yi hakan, ai hakan na nufin, ina da buƙatar kotu ta aiyanar da adalci irin nata,” in ji shi.

Tanko ya kuma baiyana cewa shi bai daddatsa jikin Hanifa da wuƙa ba kamar yadda rahotanni su ka nuna.

A cewar sa, lokacin da ta rasu, ya saka ta ne a cikin buhu kuma buhun ya yi mata kaɗan, shine ya lallanƙwasa gaɓoɓinta ya cusa ta a ciki.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a ranar Litinin ne dai a ka gurfanar da Tanko da kuma wasu mutane biyu a gaban kotun majistire da ke Gidan Murtala a kan zargin kisan na Hanifa.

Tuni dai kotun ta aike da su gidan yari kafin Gwamnatin Kano ta shigar da ƙarar a kotun da ta ke da hurumin yin shari’ar.

 

Related Articles

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button