Ma’aikacin Bankin Zenith, Mai Suna Nnamdi Godson Ya Kashe Kansa A Jahar Delta Wani.
ma’aikacin bankin Zenith mai suna Nwokorie Nnamdi Godson ya kashe kansa a garin Sapele na jihar Delta.
Mun samu labarin cewa an tsinci gawarsa a rataye a cikin tarkacen tankar ruwan inda ake zargin ya rataye kansa a unguwar Ugbeyiyi da ke garin.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya yi wani rubutu a shafinsa na Facebook amma babu wanda ya san cewa rubutun na kunar bakin wake ne.
Rubutun Da Ya Rubuta Kamar Haka; “Ba ni da tunanin kaina. Domin yanzu ina yin abubuwan da na yi nadama daga baya.
Gwagwarmayar ba ta da ban dariya kuma. Har yanzu ina da kyau a zuciya don haka ku sani. ”
Matashin wanda yake aiki a bankin Zenith, mai suna Nwokorie Nnamdi Godson, ya kashe kan sa ne ta hanyar rataya, inda kafin mutuwarsa ya sanya wadannan hotuna tare da yin rubutu a matsayin wasiyya a shafinsa na facebook.
Allah Ka Jikan Musulmai Kasa Mufi Karfin Zuciyar Mu, Kakare Mu Daga Sharrin Shedan Da Rudin Zuciya Alfarmar Shugaba S.A.W Amin