Fitaccen jarumin shirya fina finan hausa a kannywood Ali Nuhu yayi Allah wadai da kisan mutane a jahar oyo.
Jarumi Ali nuhu ya bayyana takaicin nasa a shafinsa na sada zumunta tare da yin Allah Wadai da wannan aika aikar.
Jarumin ya bayyana cewa. Kashe rayukan wadanda ba su ji ba ba su gani ba da lalata dukiyoyi a Ibadan abin takaici ne, ya kamata hukumomin da abin ya shafa su yi abin da ya kamata, hotunan da bidiyon da ake yadawa Abin damuwa ne.
StopTheBlood Adaina zubar da jini ibadanCrisis
Tun bayan faruwar Wannan lamari jarumai da dama daga masana’antar ta kannywood ke Allah wadai da wannan aika aikar.
Ciki kuwa hadda jaruma rahama sadau da jarumi Abba elmustapha dakuma falalu a dorayi da dai sauran su.
Allah ya saka mukuda alkairi allah ya yara muku yaran ku damu baki daya ameen ya hayyu ya qayyum