Religion

Ga Matakan da yakamata mace  ta dauka idan har mijinta manemin mata ne, -Sheikh Abdullahi Gadon Kaya

Ga Matakan da yakamata mace  ta dauka idan har mijinta manemin mata ne

A wannan kashi na 24 din, shirin ya yi duba ne kan matakan da mace za ta dauka idan ta samu kanta a jarabawar miji mai neman mata.

Wani babban al’amari da ke lalata aurarraki da zamantakewar ma’aurata a lokuta da dama shi ne cin amanar aure, kamar jarrabar mace da miji mai neman mata, kamar yadda malam ya fada a farkon shirin.

Irin wannan matsala ta zama sanadin mutuwar miliyoyin aurarraki a al’ummarmu, ko kuma ta saka wa wasu hawan jini ko ma ta zama silar yaduwar munanan cututtuka ga wadanda ma ba su ji ba ba su gani ba.

Sai dai abin takaicin duk da wadannan matsaloli sai a ji wasu matan da suka kallafawa ransu matsanancin kishi suna cewa wai da kishiyar gida gara ta waje. Kaico!

Sheikh Dr Abdullah Gadon Kaya, wani malamin addinin Musulunci a birnin Kano da ke Najeriya, ya yi fashin-baƙi a wannan makon kan lamarin.

Ya tabo batun yadda wasu matan kan yi sakaci har mazansu su fara yawon-ta-zubar.

Sannan ya bai wa matan da ke cikin jarabtar shawarwarin da muke fata su zama mafita, tare da gargadi ga maza masu irin wannan halin.

KU KALLI BIDIYON ANAN

https://youtu.be/5unCHItqajI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button